Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: shugaban kasar Iran Masoud Pezzekian ya bayyana a wata hira da yayi da tashar talabijin ta Aljazeera cewa, Iran a shirye take ta tunkara duk wani yunkuri na soji da gwamnatin sahyoniyawa za ta yi, kuma ikirarin ruguza shirin nukiliyar kasar Iran ba wani abu bane illa yaudarar kai.
A cikin hirarsa ta farko ta talabijin bayan kaddamar da yakin kwanaki 12 a kan Iran a ranar 13 ga watan Yuni, ya ce sojojin kasar Iran a shirye suke su kai farmaki cikin zurfin yankunan da aka mamaye.
Shugaban na Iran ya yi ishara da hare-hare masu gauni da Iran ta kai a yankunan da Isra’ila ta mamaye, ya kuma jaddada cewa Tel Aviv na boye asarar da ta yi ne.
Pezzekian ya ce: Gwamnatin sahyoniyawa tana hana watsa duk wani labari kan nasarar hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai mata, amma rokon da ta yi na dakatar da yakin shaida ce da ke bayyana hakikanin gaskiya. Isra'ila ta yi kokarin raunana da rarraba Jamhuriyar Musulunci ta hanyar haifar da hargitsi da kai hare-hare, amma ta kasa yin hakan.
Shugaban na Iran ya jaddada cewa: Iran ba ta son yaki kuma ba ta ganin tsagaita bude wutar a matsayin tabbaccen abu. Iran za ta kare kanta da dukkan karfinta. Iran ba ta mika wuya ba kuma ba za ta yi ba. Muna mai da hankali kan diflomasiyya da tattaunawa ne.
Dangane da harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran a baya-bayan nan da kuma kalaman shugaban Amurka Donald Trump na cewa wadannan hare-haren sun lalata shirin nukiliyar Iran gaba daya, Pezizkian ya dauki hakan a matsayin yaudarar kai, ya kuma ce: makamashin nukiliyar mu yana cikin kwakwalen masana kimiyyar mu ne ba a kayan nukiliya ba. Muna jaddada ci gaba da shirin nukiliyar Iran da inganta makamashin Uranium a cikin tsarin dokokin kasa da kasa.
Shugaban na Iran, yana mai nuni da cewa Tehran ba ta neman makaman kare dangi, ya jaddada cewa: Tilas ne tattaunawar da za a yi da Amurka a nan gaba ta dogara ne kan moriyar juna da samun nasara.
Pezizkian ya ci gaba da yin ishara da irin gagarumin goyon bayan da kasashen yankin suka ba Iran a yakin kwanaki 12 da gwamnatin sahyoniyawan ta kakabawa Iran, yana mai bayyana hakan a matsayin lamarin da ba a taba ganin irinsa ba.
Ya kuma kara da cewa Iran a shirye take ta samar da tsarin tsaro na bai daya tare da makwabtanta Larabawa da sauran kasashen yankin, ya kuma jaddada harin da Iran ta kai kan sansanin Al-Udeid na kasar Qatar yana mai cewa: Iran ba ta kai wa Qatar da al'ummarta hari ba, sai dai ta kai hari kan sansanin Amurka da daga cen ne ake kai hari Iran din, mun fahimci matsayi da tunanin 'yan Qatar din kuma mun tattauna da sarkin Qatar a wannan rana. Dangane da yunkurin da gwamnatin sahyoniyawan ke yi na kashe shi a yakin baya-bayan nan, Pezizkian ya ce manufar ita ce kashe manyan jami'an siyasa bayan kashe kwamandojin soji domin haifar da rudani da kifar da gwamnatin.
Your Comment